A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya taya al'ummar Iran cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin Musulunci wanda Imam Khumaini ya jagoranta.
Cikakken sakon shi ne kamar haka:
Muna taya ɗaukacin al'ummar Musulmi da dukkan ƴantattu masoya adalci na duniya murnar zagayowar ranar nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran. Yau shekara arba'in da bakwai (47) da samun wannan nasara.
Allah Ta'ala Ya kare Jamhuriyar Musulunci ta Iran; Ya kare Jagora Sayyid Qa'id Al-Imam Ali Khamenei da mataimakansa na malamai da kwamandodin mayaƙa na sama da na ruwa da na ƙasa. Muna roƙon Allah Ta'ala Ya yaɗa saƙon wannan juyi zuwa dukkan sassan duniya. Allah kuma Ya gaggauta bayyanar Qa'im, Sahibul Asr waz Zaman (Aj).
Your Comment